1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An aikata rashin imani lokacin mulkin mallakar Faransa a Aljeriya

December 20, 2012

A shekarar 1962 Aljeriya ta samu 'yancin kanta daga Faransa bayan wani mummunan yaƙi na shekaru takwas, inda ɗaruruwan rayuka suka salwanta.

https://p.dw.com/p/176Hv
Hoto: Reuters

Shugaban Faransa Francois Hollande dake ziyarar aiki a ƙasar Aljeriya, a wannan Alhamis ya yi jawabi gaban majalisar dokokin ƙasar inda ya bayyana mulkin mallakar da Faransa ta yi wa Aljeriya na tsawon shekaru 132 da cewa an bi wani tsari na rashin adalci da kuma rashin imani. Shugaba Hollande ya ƙara da cewa babu abin da mulkin mallakar na Faransa ya janyo wa al'umar Aljeriya in ban da wahalhalu. A shekarar 1962 Aljeriya ta samu 'yancin kanta daga Faransa bayan yaƙi na shekaru takwas, inda ɗaruruwan rayuka suka salwanta. A ranar Laraba shugaban na Faransa dake ziyararsa ta farko a ƙasar dake yankin arewacin Afirka, ya ƙi neman afuwa ga mulkin mallakar da ƙasarsa ta yi wa Alajeriya. A hannu ɗaya kuma Faransa da Aljeriya sun jaddada aniyar ganin an cimma buƙatar sake haƙewar ƙasar Mali ta hanyar tattaunawa amma ba tare da halarta ƙungiyoyin yan ta'adda ba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu