An alkawarta wa Somaliya taimako mai yawa
May 7, 2013Prayim Ministan Britaniya Mr. David Cameron da shugaba Hassan Sheikh Mohamud na Somaliya sune ke daukar bakoncin taron a birnin London. Lokacin jawabi ga masu neman labarai a bayan taron da ya samu wakilcin kasashe fiye da 50 da kuma kungiyoyin agaji, David Cameron, Prayim Ministan na Britaniya, matashiya yayi kan abin da yace wai ayyukan tarzoma da ta'addancin da ya zame babbar guba a zukatan matasan kasar Somalia.
"Wannan babbar barazana ce ga harkokinmu na tsaro, kuma idan muka yi ko burus da wannan barazana to kuwa za mu maimaita kura-kuran da muka yi a Afghanistan a shekarun dubu da dari tara da casa'in.
Taimakon sake gina Somaliya
Kan irin kuduri da alwashin da kasashe tajirai suka ci wa Somaliya alwashi kuma, tuni dai Birtaniya ta ci alwashin bai wa kasar dake a yankin kahon Afirka gudummawar fam miliyan goma, kwatankwacin Dolar Amurka miliyan goma sha biyar domin bunkasa harkokinta na tsaron kasa.
Haka kuma Mr. Cameron ya jaddada muhimmancin dake tare da bunkasa tattalin arzikin kasar ta Somalia, da kuma tabbatar da tafarkin demokradiyya a kasar.
Prayim Ministan na Britaniya ya zayyana irin nasarorin da suka cimma a Somaliya tun bayan taron farko da aka yi a bara.
Tabbatar da hadaddiyar kasar Somaliya
Shi kuwa a nasa jawabin, Shugaba HassanSheikh Mahmud na Somaliya, bayan godiya ga mahalarta taron, cewa yayi babban burin kasar Somaliya, shi ne ganin an tabbatar da hadaddiyar kasar Somaliya kuma zaune cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya mai dorewa.
"Wannan burin kwanciyar hankali kuwa muna fatan zai shafi fannin siyasa, tattalin arziki, da tsaro".
Shugaban na Somaliya ya tunasar da cewa hankalin duniya na zauren wannan taro to amma, al'ummar Somaliya wannan al'amari ya shafa. Shugaba Hassan Sheikh Mahmud, ya jaddada matsayinsa da gwamnatinsa a Somaliya cewa a shirye suke domin tabbatar da tafarkin demokradiyya da ya hada duka al'ummar Somaliya, karkashin tsarin da suka gabatarwa taron domin kawo sauyi a Somalia.
Mawallafi: Mohammed Sani Dauda
Edita: Mohammad Nasiru Awal