An ba Iran wa´adi a dangane da shirin ta na nukiliya
June 9, 2006Talla
Shugaban gwamnatin kasar Austria kuma shugaban majalisar zartaswar kungiyar tarayyar Turai EU, Wolfgang Schüssel ya bawa Iran wa´adin nan da tsakiyar watan yuli da ta ba da amsa akan shirinta na nukiliya da ake takaddama a kai. Mista Schüssel ya fadawa jaridar FAZ ta nan Jamus cewar dole ne gwamnatin birnin Teheran ta ba da kwakkwarar shaidar yin watsi da shirin ta na nukiliya kafin taron kolin kungiyar G-8 da zai gudana a birnin St. Petersburg na kasar Rasha. Shi ma mimnistan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi kira ga gwamnatin Iran da ta amince da tayin warware wannan rikici da kasashen nan biyar masu kujerun dindidin a kwamitin sulhun MDD da kuma Jamus suka gabatar ma ta. Bisa bayanan da hukumar dake kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta bayar a cikin wannan mako, Iran ta fara wani sabon gwajin bunkasa sinadarin uranium.