1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bai wa 'yan tawaye wa'adin ficewa daga Ghouta

Ramatu Garba Baba
March 18, 2018

Kafar talabijin a kasar Siriya ta ce dakarun gwamnati sun bai wa 'yan tawaye wani yanki da ke karkashin garin Ghouta wa'adin sa'oi don gaggauta ficewa daga garin da ake ta barin wuta don karbe iko

https://p.dw.com/p/2uXsX
Syrien Assad besucht Truppen in Ost-Ghuta
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS/Syrian Presidency

Rahoton gidan talabijin na gwamnatin ya kara da cewa an bai  'yan tawayen zuwa karfe uku na yamma agogon kasar, don ganin sun bar birnin da ya kasance tungar karshe da gwamnati ke kokarin ganin ta karbe don samun nasara a rikicin kasar na fiye da shekaru bakwai.

Wannan na zuwa ne a yayin da shugaban kasar Turkiya  Recep Tayyip Erdogan ya sanar da nasarar dakarun kasar na karbe ikon garin Afrin daga hannun mayakan Kurdawan YPG a Siriya. Shugaban a wannan Lahadin ya ce an sami galaba kan mayakan kuma yanzu an kafa tutar kasar bayan kwace birnin da aka kwashi tsawon watannin biyu ana fafatawa a tsakanin bangarorin biyu. Turkiya ta dauki matakin yakar mayakan YPG bisa zarginsu da laifin ta'addanci da kuma hadewa da Kurdawa da suka dade suna yunkurin kafa kasarsu a Turkiya.