Jana'idar tsohon firaministan Japan
September 27, 2022A wannan Talata a birnin Tokyo fadar gwamnatin kasar Japan aka yi jana'idar tsohon Firaminista Shinzo Abe na kasa, inda masu jimami da masu zanga-zanga duk suka halarta. Firaminista Fumio Kishida ya yi jawabin girmama marigayin na irin nasarorin da ya samu lokacin da yake rike da madafun ikon kasar wadda take matsayi na uku karfin tattalin arziki tsakanin kasashen duniya.
Marigayi Abe ya kasance firaminista mafi dadewa kan madafun ikon kasar ta Japan, kuma jiga-jigan mutane da sassan duniya sun halarci jana'idar da suka hada da mataimakiyar shugaban kasar Amirka Kamala Harris, da Firamnista Narendra Modi na Indiya da kuma Firaminista Anthony Albanese na Australiya.
Shi dai marigayi tsohon Firaminista Shinzo Abe na kasar Japan ya bar duniya ranar 8 ga watan Yulin wannan shekara, yana da shekaru 67 da haihuwa, lokacin da wani dan bindiga ya halaka shi yayin gangamin yakin neman zaben majalisar dattawa ta kasar.