1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buɗe bikin wasannin Olympics a London

July 27, 2012

'Yan wasa fiye da 10,000 da 'yan kallo fiye da miliyan ɗaya ne suka hallara a London inda ake wasannin Olympics na lokacin bazara na shekara ta 2012

https://p.dw.com/p/15fOo
Hoto: dapd

Shugaban jami'an tsaron cikin gida na Birtaniya da ake kira M15, Jonathan Evans, ya tabbatar da cewa akwai ƙalubale yayin gasar Olympics na birnin Londan, saboda 'yan ta'adda ka iya neman kai hari. Evans ya ce shi da sauran jami'an na aikin tabbatar da tsaro, yayin gasar na Olympics, inda Birtaniya ya fara karɓar wannan babban gasa.

Babban harin ta'addaci na ƙarshe da aka kai birnin London, shi ne akan harƙoƙin sufuri. Inda wasu masu kaifin kishin Islama suka kai harin layin dogo na ƙarƙashin ƙasa da motar safa a watan Yulin shekara ta 2005. Yayin da wannan gasa ke gudana dukkanin harkokin sufurin Birtaniya zasu kasance cikin matakan kariya. Akwai na'urorin ɗaukan hotuna fiye da 30,000 da aka jibje domin saka ido kan abubuwan dake tafiya, kuma babban jami'in 'yan sandan Birtaniya kan harkokin sufurin Andy Trotter yace akwai ɗaruruwan jami'ai aka girke:

Wannan babban kwaji ne gare mu, a matsayinmu na ƙungiya cikin tarihi. Kuma mun shirya game da duk abunda ka iya faruwa. Kuma zamu tabbatar da cewa duk abubuwa sun tafi daidai."

An ƙarfafa matakan tsaro yayin da ake sa ran kimanin mutane 600,000 suka samu ko kuma zasu samu shiga cikin wuraren gasar. Sun haɗa da 'yan guje guje da tsalle tsalle daga ciki da wajen ƙasar, da waɗanda ake kira iyalan Olympics wato jami'ai da masu ɗaukan nauyi. Baroness Neville-Jones tsohuwar Ministar cikin gida ce ta Birtaniya:

Jacques Rogge bei Olympia PK im April 2008 in Singapur
Jacques Rogge, shugaban Olympics na duniyaHoto: picture-alliance/dpa

"Duk wakilai zasu bi cikin matakan da aka tsara. Jami'an shige da ficenmu sun shiga cikin ƙasashen da zasu turo da wakilai, sun duba duk takardun wakilan da ƙasashen zasu turo."

Amma tsoron shine na 'yan ta'addan cikin gida. Filin gasar yana ƙarshen gabashin birnin na London. Kuma nan ake da mafi yawan waɗanda ake zargi da aiyukan ta'addanci tare da kame kamen da aka yi cikin shekarun da suka gabata fiye da ko wani yanki dake nahiyar Turai. Wasan ana gudanarwa cikin watan Azumin Ramadana mai tsarki ga al'umar Musulmai. Noman Benotman ya jingine haƙidan tsat-tsauran ra'ayin Islama, kuma yayi imanin 'yan ta'adda ka iya farma gasar cikin watan Azumi:

Zasu yi tunanin cewa wannan shine lokacin da ya dace, sukai harin ta'addanci, kun sani. Mai yuwuwa dama ce ta makoma mai kyau. Suna tunanin mutuwan, kisan wani, wani abu ne mai kyau, wanda kuma a gaskiya ya saɓa wa duk wata koyarwa, da duk sharudan addinin Islama, Layuwa tana da mahimmaci amma banda mutuwa.

Wannan ya zama barazana ga 'yan sanda da sauran jami'an tsaro gararamba. Ya zama wajibi su kare rayuwar mutane ba tare da sun nuna tsangwama wa Musulman da babu ruwansu ba cikin watan na Azumi. Roy Ramm shine tsohon Kwamishinan 'yan sandan birnin dake da kwarewan kan yaƙan aiyukan ta'addanci. Ya ce 'yan sandan na ƙarƙashin matsin lamba.

Wannan yana da nasaba da samun bayanan leƙen asiri. Zasu binciko waɗandak ke shirya wani abu. Idan sukayi hanzari za a yia zarginsu da wuce gona da iri, musamman cikin watan Azumi. Idan suka yi saiɓi zasu iya jefa rayuwar al'uma cikin kasada.

Olympischen Sommerspiele London 2012 Medaillen
Lambobin zinariya da azurfa da tagulla da za'a baiwa yan wasa a LondonHoto: picture-alliance/dpa

Jami'an Birtaniya na fatar matakan za su shawo kan aiyukan ta'addanci. Yayin da 'yan wasa ke rige rigen samun lambobin yabo, a ɗaya ɓangaren 'yan sanda da sauran jami'an tsaro na aikin kashe kuɗaɗen da suka kai miliyan dubu daya da rabi, domin samar da tsaro ga kowa a tsawon makonni ukku na wasannin.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar