An buɗe taron ƙasashen duniya kan tsaro a birnin Munich
February 3, 2012Yayin da aka buɗe babban taron duniya kan sha'anin tsaro karo na 48 a birnin Munich na nan ƙasar Jamus, shugaban taron Wolfgang Ischinger yayi gargaɗi game da tasirin da rikicin kuɗi na ƙasa da ƙasa ka iya yiwa harkokin tsaro. Ya ce manufar tsaro a wannan ƙarni na 21 ba ta nufin aikin kare ƙasa kaɗai, a'a ta kai ga ba da gudunmawar tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a duniya baki ɗaya. Ciki har da kyawawan manufofin raya ƙasa wanda wani lokaci yake zama tilas a girke sojoji a ƙasashen da ba na su ba, wanda hakan ke cin maƙudan kuɗaɗe. Ya ce idan ƙasashen yamma suka gaza wajen tabbatar da zaman lafiya saboda basussukan dake kansu, to da akwai haɗarin fuskantar rashin kwanciyar hankali a cikin gida. Taron da za a ɗauki kwanaki uku ana yi, yana samun halarcin wakilai 350 daga fannonin siyasa, aikin soja, tattalin arziki da kuma kungiyoyin farar hula.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi