Babban taro kan sauyin yanayi a kasar Poland
December 3, 2018Ra’ayi dai ya kusan zuwa daya a tsakanin daukacin kasashe kusan 200 da suka taru a birnin Katowice cewar fa duniya tana fuskantar barazana mai girma , kuma akwai bukatar gaggawa da nufin tunkarar annobar sauyi na muhallin da ke barazana ga ko’ina a halin yanzu.
Babban burin mahalarta taron dai na zaman samar da dabarun rage yawan amfani da sinadarin Carbon da kusan kaso 45 nan da shekaru 12 da ke tafe sannan kuma da kai karshensa gaba daya zuwa shekara ta 2050 in Allah ya so.
Duniyar dai na fatan karkata zuwa ga makamashi irin na hasken rana da ba’a bukatar konashi duk a cikin neman mafitar kara dumamar da ke zaman barazana mai girman gaske a cewar Antonio Gutteras dake zaman sakataren Majalisar Dinkin Duniya kuma daya a cikin masu jawabi yayin bude taron.
“Aikinmu a nan a Katowice shine kai karshendabarun aiwatar da yarjejeniyar birnin Paris . kuma ina son in tunawa kowa cewar wannan alakwari ne muka dorawa kanmu da kuma ya kamata mu cika shi.”
Lamarin da ke bukata ta kudi. To sai dai kuma tuni Bankin Duniya ya ba da sanarwar ninka yawa na kudaden da yake kashewa a bisa harkar ta muhalli daga Dalar Amirka miliyan dubu 20 ya zuwa dubu 200 a cikin shekaru biyar din da ke tafe.
Ana dai samun rarrabuwa a tsakanin kanana na kasashe da ke jin a jikin matsalar duk da kasancewarsu kurar baya a kaiwa zuwa ga haifar da ita, da kuma ‘yan uwansu manya da tuni suka fice daga yunkurin rage amfani da makamashin na Carbon.
Babu dai manya na kasashe irin Amirka da ke na kan gaba a cikin dumamar yanayin da kuma daga dukkan alamu ke da rawar takawa da nufin kai karshen matsalar da ta haifar da ambaliyar ruwa da guguwa a wasu wuraren sannan kuma da rigingimu irin nasu makiyaya da manoma a kasashe irin Najeriya.
Abun kuma da a fadar Frank Bainimarama da ke zaman firaministan Fiji kuma shugaban taron da ke barin gado ya sa hada kai zaman a wajibi a tsakanin kowa.
To sai dai in har kanana na kasashe irin nasu Fiji na ganin babu lokacin batawa, ga manya irin nasu Poland da ke karbar baki da kuma a bana kadai ta yi asarar kusan Dalar Amirka miliyan 800 sakamakon wani farin da ake ta'allakawa da sauyin na muhalli, lokacin yanke hukuncin bai wuce yanzu ba a cewar Firaminista Mateusz Morawiecki na Poland kuma sabon shugaban taron karo na 24.
Ana dai sa ran share kusan tsawon wannan mako ana yamutsa gashin baki da tafka dogon Turanci da nufin kai wa matsayin da yake iya dadi ga kanana da manya na kasashen da ke a zauren taron.