An bude gasar wasannin Olympics a hukumance
August 5, 2016An dai yi shagulgula masu kayartawa a wani bangare na fara gasar. Ana ci gaba da nuna fargaba kan batun tsaro, to sai dai hukumomin kasar Brazil sun ce sun shirya tsaf don ganin ba a samu wata matsala ba.
An kara daukar matakan tsaro gabannin wasannin
Jami´an 'yan sandan kasa da kasa daga kasashen Faransa da Beljiyam da Canada da Amirka ne suke halartar bikin bude gasar ta Olympic don sanya ido daga lokacin da aka fara gasar har zuwa kammalawa a wani mataki na taimaka wa Brazil kammala wasanin ´yan kallo lafiya mai wasa lafiya. Ministan shari´a na Brazil Alexandre Moraes, ya ce an samar da cibiyar aiyyukan 'yan sandan kasa da kasa.
Ya ce"mun hada gwiwa da kasashen duniya inda jami´an tattara bayanan sirri na Brazil za su hadu a Braziliya inda daga nan ne za´a rika sanya idanu kan abubuwan da suke tafiya lokacin wasannin na Olympic"
Kasar Brazil mai masaukin baki ta horas da jami´an 'yan sanda na cikin gida da na kasashen waje, musamman wadanda suka kware wajen yaki da ta´addanci. Inda kuma aka girke dakarun tsaron kimanin 21,000 da suka hada da 'yan sanda da sojoji a filayen wasanni daban-daban da tashoshin jiragen kasa da na sama da otel-otel da kuma manyan hanyoyi, a wani mataki na murkushe duk wani hari da 'yan ta´adda ka iya kai.Kazalika rahotanni sun bayyana cewa jami´an tsaro za su ci gaba da kasancewa a birnin Rio ko bayan kammala gasar, saboda abin da ka je ya zo.
Hukumar FBI ta Amirka na taimakawa wajen tabbatar da tsaro a wasannin
A watan da ya gabata sai da hukumomin kasar Brazil da taimakon hukumar bincike ta FBI suka kama mutane 12 da ake zargi da kokarin taimaka wa kungiyar IS wajen kai hare-hare a lokacin wasannin, wadda kuma hakan ke ci gaba da sanya shakku kan ingancin tsaron da aka shirya.Robert Muggah mai sharhi ne kan harkokin tsaro, ya ce an kashe sama da dala miliyan 550 don samar da tsaro, muna fatan kwalliya za ta biya kudin sabulu.
Ya ce"akwai hukumomin tsaro har kimanin 55 da biyar da za su taimaka, amma tilas sai jami´an farin kaya sun yi aiki da sojioji da 'yan sanda lokaci guda don a samu nasara."
Sai dai baya ga wadannan abubuwa, akwai batun sata da kwace-kwace a titunan Brazil musamman a guraren shakatawa da ma batun cutar Zika, lamarin da ya sanya wasu 'yan wasa suka kauracewa gasar, to sai dai hukumomin kasar sun ce sun dauki matakan kare yaduwar wannan cutar da kuma dakile duk wani yunkuri na aikata ba dai-dai ba.