1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude sabon babin siyasa a Pakistan

Ibrahim SaniNovember 15, 2007
https://p.dw.com/p/CHoY

Shugaba Pavez Musharraf na Pakistan ya naɗa Mr Mohammed Soomro , a matsayin Faraministan wucin gadi a ƙasar. A cewar Mr Musharraf, sabon Faraministan zai jagoranci zaɓen ´Yan Majalisun dokokine da ake shirin gudanarwa a ƙasarne.Shugaban na Pakistan ya kuma tabbatar da cewa, a ranar ɗaya ga watan Disamba na wannan shekara, zai ajiye muƙaminsa na shugaban sojin ƙasar. A yau Alhamis dai wa´adin ´Yan Majalisun dokokin ke ƙarewa. A waje ɗaya kuma tsoffin Faraministocin ƙasar biyu, wato Benazir Bhutto da Nawaz Sharif sun cimma yarjejeniyar aiki tare, don kalubalantar Mr Musharraf a fagen zaɓen. A yanzu haka dai Benazir Bhutto na ci gaba da kasancewa a cikin ɗaurin talala, a wani gida dake gabashin birnin Lahore. Shi kuwa Nawaz Sharif na gudun hijirane a ƙasar Saudiya.