An bude taron duniya kan harkokin tsaro a birnin Munich
February 10, 2007Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce a shirye gamaiyar kasa da kasa ta ke ta hana Iran kirkiro wani shiri na kera makaman nukiliya. Merkel ta fadawa taron kasashen duniya kan harkokin tsaro a birnin Munich cewa dole ne gwamnati a Teheran ta amince da bukatun MDD da na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA.
“A saboda haka dole ne Iran ta cike kudurin kwamitin sulhun MDD da na gwamnonin hukumar IAEA. Babu wani zabi bayan haka, kuma babu wani kace nace ko wata dubara.”
Shi kuwa a jawabin sa ga taron shugaban Rasha Valdimir Putin cewa yayi amfani da karfin soji da Amirka ke kara yi na kirkiro wata sabuwar tserereniyar kera makamai. Putin ya ce haka na karfafa guiwar kananan kasashe wajen kera makaman nukiliya. Sakataren tsaron Amirka Robert Gates da babban mai shiga tsakani na Iran a shawarwarin da ake yi game da shirin ta na nukiliya Ali Larijani na cikin manyan kusoshin ´yan siyasa sama da 40 dake halartar taron na Munich. Rahotannin farko sun nunar da cewa Larijani ba zai iya halartar taron ba sabaoda dalilai na rashin lafiya. An sa rai zai gana da ministan harkokin wajen Jamus F-W Steinmeier da babban jami´in diplomasiyar KTT Javier Solana a gefen taron.