1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude taron sasanta rikicin Siriya a Geneva

Gazali Abdou TasawaJanuary 29, 2016

Tawagar wakillan gwamnati da na 'yan tawayen Siriya sun hallara a taron neman shawo kann rikicin Siriya wanda kasashen duniya ke gudanarwa a birnin Geneva a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya

https://p.dw.com/p/1Hm3s
Genf Friedensverhandlungen zu Krieg in Syrien
Hoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

A wannan Jumma'a ce a birnin Geneva aka bude taron kasashen duniya kan neman shawo kan rikicin kasar Siriya a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya. Rahotannin daga birnin na Geneva na cewar tawagar gwamnatin kasar Siriyar mai kunshe da mambobi 16 a karkashin jagorancin jakadan kasar ta Siriya a Majalisar Dinkin Duniya Bachar al-Jaafari ta isa a birnin na Geneva da yammacin wannan Jumma'a, kuma nan gaba kadan za ta gana da manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniyar a kasar ta Siriya Staffan Mistura, ganawar da za ta kasance matakin farko da soma tattaunawar.

Su ma dai daga nasu bangare 'yan adawar kasar ta Siriya wadanda da farko suka yi watsi da tayin halartar taron sun bada sanarwar shirin aiko da wata takaitacciyar tawaga ta mutane uku a taron na birnin Geneva wadanda amma ba ta ba su hurumin shiga tattaunawar ba kai tsaye ba.Za a dai share watannin shida ana gudanar da wannan taro da nufin kawo karshen yakin kasar ta Siriya wanda kawo yanzu ya yi sanadiyayar mutuwar mutane sama da dubu 260 tare da jefa wasu miliyoyin 'yan kasar cikin gudun hijira