1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hana jirage sauka a Saliyo

Abdul-raheem Hassan
November 26, 2023

Dakarun kasar Saliyo sun murkushe yunkurin harin ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a kan barikin sojoji, tare da rufe sararin samaniyar kasar baki daya.

https://p.dw.com/p/4ZSBb
Jami'an sojan gwamnatin SaliyoHoto: Jean-Philippe-Ksiazek/picture-alliance/dpa

Sanarwar da gwamnatin ƙasar ta fitar ya bukaci 'yan ƙasar da su zauna a cikin gida yayin da jami'an tsaron cikin gida ke daukar matakan da suka dace.

Wani babban jami'in gwamnati da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an fasa babban gidan yari da ke birnin Freetown, kuma wasu fursunoni sun tsere. Gidan yarin wanda aka tsara don ɗaukar fursunoni 324, yana cunkushe da fursunoni 2,000 a shekarar 2019 a cewar rahoton ma'aikatar harkokin wajen Amirka.

Ba a bayyana adadin fursunonin da suka tsere ba zuwa yanzu, amma wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna mutane da dama sun gudu daga gidan yarin, yayin da ake jin karar harbin bindigogi. Kamfanin dillancin labaran reuters bai tantance faifan bidiyon ba.

Kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta yi Allah wadai da abin ta kira yunkurin wasu mutane na "samun makamai da kawo cikas ga tsarin mulki" a Saliyo. Wata sanarwa daga ofishin jakadancin Amirka a Freetown ya yi tir da abin da ya faru.

Rikicin siyasa a ƙasar Saliyo da ke Afirka ta Yamma yana dada rincabewa tun bayan sake zaben Shugaba Julius Maada Bio a zabe mai cike da takaddama a watan Yuni, wanda babban adan Adawa ya yi watsi da sakamakonsa.

Zanga-zangar adawa da gwamnati ta yi sanadiyar mutuwar mutane shida, 'yan sanda da akalla fararen hula 21 a watan Agustan 2023. Yanzu haka dai kasashe takwas ke cikin juyin mulkin sojoji a yammacin Afirka da tsakiyar nahiyar tun daga shekarar 2020, matakin da ke nuna komaya ga dimukuradiyya.