An bude wuta a kan jami'an sa ido na kungiyar OSCE a Ukraine
November 20, 2014Talla
Masu sa ido na kungiyar tsaro da hadin kai a Turai OSCE sun ce wasu mutane cikin kayan sarki sun bude wuta a kan wani ayarin motocinsu a gabacin Ukraine. Ayarin dai na masu sa ido ne a kan shirin tsagaita wuta a yankin da ke fama da rikici da ke kusa da garin Maryinka. Sai dai ba wanda ya jikkata a wannan lamari. Yankin mai nisan kilomita 15 yamma da Donetzk tungar 'yan aware, yana karkashin ikon sojojin Ukraine ne. Tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wutar a farkon watan Satumba ake karya ka'idojinta. Alkalumman da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar sun nuna cewa mutane kimaninn 1000 aka kashe a gabacin Ukraine tun bayan amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a hukumance.