An cafke Charles Taylor
March 29, 2006Talla
Jamian yan sanda a Najeriya sun damke tsohon shugaban kasar Liberia,a bakin iyaka Najeriya da Kamaru.
Charles Taylor ya bace ne tun ranar litinin,bayan shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo,ya bada umurnin mayar da Taylor kasarsa Liberia.
Kotun kasa da kasa dake sauraron laifukan yaki dake Saliyo,take neman Charles Taylor bisa laifukan yaki 17 .
Yanzu haka da Obasanjo dake ziyara kasar Amurka ya bada umurnin maiyarda Taylor gida ba tare da bata lokaci ba.