1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cafke matasan da ake zargi da hallaka 'yan majalisa biyu a Kano

January 2, 2013

Rundunar 'yan sandar jihar Kano ta gano masu alhakin aikata ta'adin kisan kai.

https://p.dw.com/p/17CcH
Polizeiposten und gesperrte Straßen prägen den Alltag in der Millionenstadt Kano. Copyright: Katrin Gänsler Kano, Nigeria, 06.02.2012
Hoto: Katrin Gänsler

Rundunar 'yan sandan a jihar Kano, ta ce ta cafke mutanen da take zargi da hannu wajen hallaka 'yan majalisun dokokin jihar biyu a 'yan kwanakin nan.

A wannan Laraba, kwamishinan 'yan sandan jihar, Alhaji Ibrahim Idris, ya nuna wasu mutane biyu da suka haɗa da wani matashi mai suna Ibrahim Lawal, ɗan shekaru 22, wanda rundunar ta bayyana shi a matsayin ɗaya, daga cikin gungun 'yan ta'adda da suka aikata wannan kisan kai.Haka kuma, rundunar ta ce shugaban ƙungiyar 'yan kasuwar sabon garin Kano ta AMATA Alhaji Saleh Kura, shine ya biya matasan, wajen hallaka 'yan majalisun kamar dai yadda komishinan Ibrahim Idris ya baiyana
Clip Idris:
Sai dai kuma waɗanda ake zargin sun ce ba su da wani hannu cikin wannan kisa.

Mawallafa: Nasir Salisu Zango/ Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu