An cafke tsohon Shugaban mulkin Soja na Kasar Pakistan
April 25, 2013An cafke tsohon Shugaban mulkin Soja na Kasar Pakistan Pervez Musharraf bisa zarginsa da Kasahe tsohuwar Firayim Ministan Kasar Benezir Bhutu.
Masu gabatar da kara sunce kisan Bhutu shine na biyu daga cikin laifuka uku da ake tuhumar sa da aikatawa a yayin da yake kan karagar mulki daga Shekara ta 1999 zuwa 2008.
An dai kama tsohon Shugaba Musaharraf ne kwana guda bayan da wata kotu A pakistan taki amincewa ta kara bada belinshi.
Kame Musharraf da kuma kin amincewa da ya tsaya takarar shugabancin Kasar a zaben da za'a gudanar ranar 11 ga watan mayu mai zuwa ya zamo wani babban kalubale ga tsohon shugaban da ya dawo Pakistan a watan daya gabata yana mai alwashin cewa ya dawo ne domin ya ceto kasar.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu