1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda sun kama wasu 'yan Kaar Jamus a Masar

Abdourahamane Hassane
January 11, 2019

An kama wasu 'yan Kasar Jamus guda biyu a Masar wadanda ake zargi suna da niyar isa a yankin Sinai domin shiga jihadi a cikin kungiyar IS.

https://p.dw.com/p/3BQP0
Ägypten Symbolbild Prozess gegen Muslimbrüder
Hoto: picture alliance/dpa/K. Elfiqi

Wasu majiyoyin tsaro na Masar sun ce tuni da aka fara kokarin sake tisa keyar matasan zuwa Jamus. Na farko wanda aka kama Mohammed A dan shekaru 24 an kamashi ne a cikin watan Disamba da ya gabata a filin saukar jiragen sama na birnin Alkahira. Yayin da na biyu wanda dan shekaru 18 ya kai ziyara ganin kakansa a cikin watan Disamba bara a birnin Alkahira amma kuma tun lokacin bai sake komawa Jamus ba.