1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An ceto bakin haure a Tunisiya

June 27, 2021

A wannan Lahadin, gwamnatin Tunisiya ta sanar da kubutar da wasu masu tafiyar kasada zuwa manyan kasashen duniya ta barauniyar hanya, inda wasu ma suka salwanta.

https://p.dw.com/p/3veM4
Tunesien Boot mit 125 illegalen Einwanderern wurde gerettet
Hoto: Tasnim Nasri/AA/picture alliance

Ma'aikatar tsaro a Tunisiya, ta ce sojojin ruwan kasar sun ceto wasu bakin haure su 178, mutanen kuma da ke kokarin shiga kasashen Turai ala kulli halin.

Jami'ai sun ce sun gano gawarwakin mutane biyu daga cikin bakin na haure, a wani sintiri na musamman da suka kaddamar a gabar ruwan da ke a kudancin kasar.

Masu tafiyar ta kasada dai, galibi sun fito ne daga kasashen Tunisiya da Masar da Siriya da Najeriya da Mali da Bangaladash da ma kasar Ethiopia wato Habasha.

Ko a ranar Alhamis da ta gabata ma hukumomin Tunisiyar sun ce sun kama wasu sama da mutum 260 da ke yunkurin fadawa tekun Bahar Rum bayan barin kasar Libiya, kuma galibin su 'yan kasar Bangaladash ne.