Burkina Faso: An ceto mata 62 da aka sace
January 21, 2023Talla
Hukumomi a Burkina Faso sun ce an ceto mutanen ne bayan wani gagrumin samame da rundunar tsaron kasar ta aiwatar, sai dai ba wani karin haske kan yadda aka samo matan. Gidan talabijin din Burkina Faso (RTB) ya nuna yadda wata mota ta kwaso matan da jariransu, da yadda aka danka su a hannun hukuma. A tsakiyar wannan watan ne gwamnatin Burkina Faso ta zargi mayakan jihadi da sace mata 62 da jariransu hudu a yankin Arbinda na lardin Soum da ke arewacin kasar, yankin da hare-haren mayakan da ke ikrarin jihadi ya daidaita.