An ceto mutane 24 a cikin saharar Nijar
June 27, 2017Talla
Mukaddashin gwamnati a garin Bilma na arewacin kasar Fatoumi Boudou, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mutanen da aka ceton sun sanar da cewa su 70 zuwa 75 aka dauko su a cikin motoci uku daga garin Agadez zuwa kasar Libiya. Haka nan kuma da dama daga cikinsu sun mutu kan hanya bayan da masu safarar tasu suka gudu suka bar su a tsakiyar Sahara.
Wani gidan radiyon garin na Bilma ya sanar a jiya Litinin cewa daga baya jami'an sojin kasar ta Nijar sun sake yin nasarar tsinto gawarwakin mutane 52 a cikin dajin Saharar.