1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ceto 'yan gudun hijira sama da dubu a teku

Gazali Abdou Tasawa
January 17, 2018

Jami'an tsaron gabar ruwan kasashen Italiya da Spain sun sanar da ceto 'yan gudun hijira 1.400 daga kasashen Arewacin Afirka a tekun Baharum a jiya Talata.

https://p.dw.com/p/2qxSd
Libysche Küste, Rettungsboot mit Flüchtlingen
Hoto: Getty Images/A.Paduano

Wasu jiragen ruwa na hadin gwiwar jami'an tsaron gabar ruwan kasar ta Italiya da rundunar yaki da fataucin bakin haure ta Kungiyar Tarayyar Turai  ta Sophia da kuma Kungiyar Proactiva mai zaman kanta ta kasar Spain sun gudanar da sawu 11 a cikin tekun wajen ceto bakin hauren da suka fito daga kasashen arewacin Afirka.

Bakin hauren sun hada da mata 175 da kananan yara 75 wadanda ke tsattsage a cikin jiragen kwale-kwale marasa inganci guda bakwai inda masu ayyukan ceto suka tarar da gawar wani dan karamin yaro da ya mutu a cikin tafiyar tasu. 

Kazalika wasu jami'an ceto na Spain sun ceto wani jirgi makare da 'yan gudun hijirar kimanin 400 a cikin wani yanayi mai cike da hadari inda nan ma suka iske gawar wani karamin yaro daya.