1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

281211 Mubarak Prozess

Mohammad AwalDecember 28, 2011

Hosni Mubarak dai na fuskantar hukuncin kisa sai dai ana zargin cewa ba za a yi adalci ba domin mutanensa ke yi masa shari'a.

https://p.dw.com/p/13b3a
epa03044247 Anti-riot soldiers and army forces (background) stand guard outside the police Academy during the trial of former Egyptian president Hosni Muabrak in Cairo, Egypt, 28 December 2011. Tight security measures were imposed outside the police academy coordinated by the army and the Interior Ministry. More than 5,000 military and police personnel have been deployed to maintain security inside and outside the courtroom. The trial of Mubarak was resumed after a suspension of three months. Mubarak, 83, is being tried on charges of ordering the killing of around 850 people during the revolt that eventually toppled him in February. Ex-interior minister Habib al-Adli and six former security aides face the same charges, while Mubarak's sons, Alaa and Gamal, are charged with corruption. EPA/KHALED ELFIQI +++(c) dpa - Bildfunk+++
An girke dubban 'yan sanda domin gadin harabar kotunHoto: picture-alliance/dpa

Bayan katse zaman sauraron shari'a tsawon watanni uku, a wannan Laraba a birnin Alƙahira na ƙasar Masar aka ci-gaba da shari'ar da ake wa tsohon shugaban ƙasa Hosni Mubarak, wanda ake tuhumarsa da laifin ba da umarnin kashe masu zanga-zanga a lokacin boren nan na juyin juya halin ƙasar ta Masar. Masu gabatar da shari'a na kuma zarginsa da cin hanci da rashawa.

A wannan karon ma an kai tsohon shugaban ƙasar ta Masar Hosni Mubarak kotu ne akan gadon marasa lafiya. Masu adawa da Mubarak da dangi waɗanda aka kashe a lokacin boren ƙin jininsa, sun gudanar da zanga-zanga a gaban kotun dake a wajen birnin Alƙahira suna masu zargin cewa shari'ar dodorido ce kawai domin har yanzu mutanensa ke kan mulki. A daura da su akwai magoya bayan Mubarak waɗanda suka je kotun domin marasa baya yayin da aka girke 'yan sanda fiye da 5000 domin gadin ginin kotu. A baya dai an sha samun taho mu gama tsakanin magoya bayansa da masu adawa da shi.

Hamad El-Aouni masanin ƙasar Masar ne a wata jami'a dake birnin Berlin ya ce Masar ba ta da kyakkyawan tsarin shari'a.

"Ai Mubarak ne ya naɗa alƙalan babbar kotun ƙasar, kuma kasancewa babu wani tsarin shari'a mai zaman kansa a Masar, wato kenan shari'ar da ake wa Mubarak, shari'a ce kawai ta siyasa."

Ana iya yanke wa tsohon shugaban na Masar mai shekaru 83 wanda kuma shafe shekaru 30 akan mulki hukuncin kisa, idan aka tabbatar da aliafin da ake zarginsa da aikatawa wato ba da umarnin kashe mutane kimanin 850 lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa a farkon shekara 2011. Sai dai lauyansa Yasser Abdel-Razak ya ce Mubarak bai aikata wani laifi ba, ƙoƙari ake a shafa masa kashin kaji.

A man holds a placard depicting ousted President Hosni Mubarak with Arabic writing that reads, "trial of the people," in front of a courtroom in Cairo, Egypt, Wednesday, Dec. 28, 2011. Egypt's ousted leader Hosni Mubarak has been brought back into a Cairo's courtroom for the resumption of his trial after a three months' break. Mubarak is charged with complicity in the deaths of nearly 840 protesters in the crackdown against a popular uprising, which ended with his ouster on Feb. 11. He could face the death penalty if convicted. (Foto:Ahmed Ali/AP/dapd)
Masu adawa da masu goyon bayan Mubarak sun yi zanga-zanga a gaban kotunHoto: dapd

Kawo yanzu shaidun da aka gabatar a kotu sun wanke Mubarak. Hatta Fieldmarshall Mohammed Tantawi shugaban majalisar mulkin sojin ƙasar ya ce Mubarak bai ba da umarni a buɗe wuta akan masu zanga-zanga ba.

Shari'ar da ake wa Mubarak da 'ya'yansa Alaa da Gamal da tsohon ministan cikin gida Habib al-Adli da wasu jami'an 'yan sanda shida an katse ta tsawon watanni uku, domin ba wa kotun damar nazari akan ƙarar da wani lauya ya ɗauka na ƙalubalantar alƙalin shari'ar Amed Rafaat wanda lauyan ya ce ya taɓa aiki ƙarƙashin Mubarak. Yanzu haka dai ana zaman sauraron shari'ar ne a bayan idon jama'a. Ko da yake an ba wa masu sa ido kan shari'ar izinin shiga amma ba za su iya ba da rahotanni dalla-dalla game da shari'ar ba, abin da Ronald Meinardus shugaban gidauniyar Friedrich-Naumann a Alƙahira ya ce sojoji na katsalanda a cikin shari'ar.

"Shugaban majalisar soji Fieldmarshall Tantawi ya kasance mai biyayya ga Mubarak tsawon shekaru 20, musamman a matsayin ministan tsaro. Baya ga haka ilahirin 'ya'yan majalisar sojin mutane ne da suka taɓa yin biyayya ga Mubarak, shi ya sa da wuya a yi adalci a shari'ar."

Masharhanta dai na ganin mahukuntan Masar za su so akai ga yanke hukunci ba, domin Mubarak mai shekaru 83 kuma yake fama da rashin lafiya, ta Allah tana iya kasancewa akansa kafin a gama zaman sauraron shari'ar.

Mawallafa: Nils Naumann / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal