1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma yarjejeniya tsakanin yan adawa da gwamnatin Togo

Yahouza Sadissou MadobiAugust 21, 2006

Shugaba Blaise Campaore na Burkina faso,ya yi nasara sasanta rikcin siyasar Togo

https://p.dw.com/p/Btye

Kwaliya ta biya kuɗin sabulu, a tantanawar da ta haɗa gwamnati da yan adawar ƙasar Togo, a birnin Ouagadougou na Burkina Faso.

An fara tantannawa tsakanin ɓangarorin 2, tun 21 ga watan Aprul na wannan shekara, amma a ka watse baram-baram ,ba tare da cimma burin da a aka sa gaba ba.

Sai ranar 8 ga watan da mu ke ciki, Jam´iyun adawa da gwamnati, da kuma wakilan ƙungiyoyin fara hulla, su ka ɗorawa shugaban Burkina Faso Blaise, Campaore yaunin shiga tsakani.

Bayan kwanaki 10 na masanyar ra´yoyi, ɓangarori sun cimma tuidun dafawa, a kan daftarin da zai kawo ƙarshen rikicin siyara, a ƙasar Togo da ya ɗauki tsawan shekaru 12.

Daga cikin tanade-tanaden da yarjejeiniyar ta cimma, akwai batun girka gwamnatin haɗin kan ƙasa, da za ta ƙunshi yan adawa da jami´yu masu riƙe da ragamar mulki, da kuma shirya zaɓen yan majalisun dokoki, kamin watan oktober na shekara ta 2007, wato wa´adin ƙarshe, na Majalisa mai ci yanzu.

A ɗaya hannun, mahalarat taron Ouagadougou,sun amince a girka hukumar zaɓe mai zaman kanta, da zata ƙunshi wakilai 19, da su ka haɗa da 5 na ɓangaren jam´i yu masu riƙe da ragamar mulki, sannan jam´iyun adawa 5 na ƙasar, ko wace ta tura wakilai 2,sai kuma wakilai 2, na ƙungiyoyin fara hulla, da 2 na gwamnati.

Yarjejeniyar ta umurci hukumar zaɓe mai zaman kanta, ta bada fifiko ga neman sulhu, a dukan ƙudurorin da zata ɗauka.

A yayin da gamna da yan jarida, kakakin jam´iyun adawar Togo, Patrick Lawson, ya bayana gamsuwa da wannan yarjejeniya, da ya danganta a matsayin, babban mataki na kai ga tudun mun tsira.

A wani sashen kuma, yarjejeniyar da ka rataba ma hannu, ta soke batun hanna tsayawa takara zaɓen shugaban ƙasa, ga yan Togo, masu ɗauke da kati zama yan assulin wata ƙasa ta daban.

An ɗauki wannan mataki, bisa buƙatar jam´iyar UFC ta Gildchrist Olympio , wanda doka ta haramta ma shiga takara ,a dalilin da ya na ɗauke da katin ƙasar France.

Kazalika, kakakin jam´iyar RPT mai riƙe da ragamar mulki Pascal Badjona,ya nuna matuƙar gamsuwa, da sakamakon tantanawar Ouagadougou, ya kuma godiya da ban girma da shugaba Blaise Campaore, da ya samu wannan nasara.

Ranar jiya ne, a birnin Lome na ƙasar Togo, aka yi bikin ƙaddamar da wannan yarjejeniya da aka cimma, tare da halartar wakilai daga sassa daban-daban na Afrika, da kuma na ƙungiyar ECOWAS, da Taraya Afrika.

A lokacin da ya yi jawabi albarkacin bikin ƙadamarwar shugaban Togo Faure Yasimbe, ya yi kira ga ɓangarorin daban-daban, da su mutunta wannan yarjejeniya mai tarihi, wadda kuma itace babban sharaɗi ,da ƙasashen turai su ka gindaya, kamin su maida hulɗoɗi da Togo, da su ka kaste tun shekaru fiye da 10 da su ka gabata.

A nasa ɓangare, shugaba Blaise Campaore, da ya jagoranci yarjejerniyar, ya bukaci ƙungiyar gamayyya turai, ta bada tallafi domin cimma burin da aka sa gaba, kazalika ,ta amince da sake ƙulla hulɗoɗi da ƙasar Togo.

A halin yanzu dai, masu kula da al´ammura siyasa, a ƙasar na bayana cewar kar a yi saurin yaban ɗanyan mai, domin an sha rattaba hannu, akan yarjeniyoyi tsakanin yan adawa da gwamnatin Togo, amma kuma, a wayi gari ,a koma gidan jiya, noman goje.