An dage dokar ta baci a garin Rangoon dake Burma
October 20, 2007Gwamnatin sojin kasar Burma ta dage dokar ta bacin data kakaba a babban birnin kasar, wato Rangoon.Sojin sun saka dokar ta bacin ne bayan gagarumar zanga zanga da yan adawa suka dingi yine a kasar na Allah wadai da gwamnati. Masu radin dimokradiyya a kasar na muradin ganin kasar ta dawo tafarkin dimokradiyya ne, bayan tsawon shekaru 45 kasar na karkashin mulkin soji.A yanzu haka dai gwamnatin na ci gaba da tsare da dama daga cikin yan adawa na kasar, da aka cafke a lokacin zanga zangar. Ya zuwa yanzu dai tuni Amurka tabi sahun kungiyyar Eu, wajen kakabawa kasar ta Burma takunkumi. Matakin ya hadar da tsauraran dokokin shigi da ficin kaya daga Amurkan zuwa Burma. A hannu daya kuma da tsauraran matakai na bada izinin shiga Amurka daga bangaren yan kasar.