Jamus ta yi kashedi ga Hong Kong
July 31, 2020Talla
A cikin wata sanarwa da ministan harkokin waje na Jamus Heiko Maas ya bayyana ya ce dage zaben da shekara guda saboda corona. Bayan da aka haramta wa 'yan takarar jam'iyyar masu fafutukar neman sauyin na demukaradiyya tsayawa takara tare da kama wasu shugabannin kungiyoyin dalibai da kuma tilasta wa jagoran 'yan adawar yin hijira. Wani abu ne da ke zaman karan tsaye ga yankin wanda ke fafutukar neman 'yanci daga China domin tabbatar da tsari na demukaradiyya.