1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dakatar da bore a Pakistan

November 3, 2018

Masu zanga-zangar nan da ke da tsananin kishin addini a Pakistan, sun kawo karshen boren da suke yi a kasar bayan cimma yarjejeniya da gwamnati.

https://p.dw.com/p/37bVx
Pakistan Protest nach Aufhebung von Todesstrafe für christliche Frau in Lahore
Hoto: Reuters/M. Raza

Dubban mutanen da suka yi ta yin bore bayan sakin matar nan da ta yi wa addinin Islama batanci, sun mamaye tare da toshe manyan hanyoyin biranen Pakistan din ne cikin 'yan kwanakin nan.

A ranar Larabar da ta gabata ne suka fara zanga-zangar, bayan kotun kolin kasar ta saki Asia Bibi, wadda da ma ke zaman hukuncin kisa, bayan share shekaru takwas a gidan yari. 

Masu boren sun kai ga halatta jinin alkalan da suka yanke hukuncin sakin matar.

Batun batanci ga addini dai wani al'amari ne da ke zama babban laifi a Pakistan, kasar da ke da rinjayen al'umar musulmi a cikinta.