An dakatar da jam'iyyu 12 a Chadi
February 8, 2018Ministan tsaron cikin gida a kasar Chadi Ahmat Bachir, ya ce gwamnati ta haramta duk wata zanga-zanga ko ta wace irin siga a dukkanin fadin kasar, kuma duk wata jamiyar siyasa ko kungiyoyin farar hula da tayi kiran al'umma zuwa zanga-zanga, zai rasa aikinsa tare da gurfanar da ita a gaban kotu.
Ma'aikatar cikin gidan kasar ta dauki matakin haramta ayyukan wasu gamayyar jam'iyu 12, saboda sun bijire wa umarnin gwamnati na hana zanga-zanga. Amma duk da haka kungiyoyin kwadago na kan bakansu na shirya gudanar da zanga zangar lumana a kasar Chadi, gangamin da aka yi wa lakabi da "Wani hali ake ciki."
Sai dai zanga-zangar ba ta yi tasirin azo gani ba, ganin yadda jami'n tsrao suka dau kwararan matakan tsaro, amma duk da haka kungiyoyin fararen hulan sun gabatar da jawabansu a ofishohin magadan gari da ke babban birnin kasar N'Djamena.
Bisa ga alamu matsi da tsadar rayuwa ya taka muhimmiyar rawa wajen hana tasirin zanga-zangar, inda wasu rashin ci maka ya tilastasu zuwa harkokin kasuwancinsu. Sai dai a Kudancin kasar Chadi ana fama da karancin kulawar ma'aikatan jinya sakamakon shiga yajin aikin da suka yi kwanakin baya.
A yanzu dai matakan da hukumomin gwamnatin suka dauka na dakatar da ayyukan jam'iyyu 12 a kasar na tsawon watanni biyu, na a wani matakin na yunkurin ladabtar da jam'iyyun da ke shirin ja da gwamnati. Wannan ba shi ne karon farko da gwamnatin Chadi ke shiga takun saka da kungiyoyin ma'aikatu kasar ba sakamakon rashin biyan albashi, abin da ya haifar da yajin aiki a yawancin ma'aikatun gwamnati.