1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dakatar da Pakistan daga ƙungiyar Commonwealth

November 23, 2007
https://p.dw.com/p/CSCD
Ƙungiyar ƙasashen da suka taɓa zama ƙarƙashin mulkin mallakar Birtaniya wato Commonwealth ta dakatar da Pakistan daga cikin ta saboda dokar ta-ɓaci da aka kafa a ƙasar. Wani kwamitin ministocin harkokin waje ya yanke shawarar dakatar da Pakistan ɗin daga ƙungiyar har sai an maido da tafarkin demokuradiyya, inji babban sakataren Commonwealth Don McKinnon a birnin Kampala. A yau juma´a shugabannin kungiyar mai membobi kasashe 53 ke fara taron koli a babban birnin na Uganda. Pakistan ba ta cike wa´adin da kungiyar ta ba ta zuwa jiya alhamis na ta ɗage dokar ta ɓacin ba.