An dakatar da shugaban FIFA da takwaransa na UEFA
October 8, 2015Kwamitin da'a na hukumar kwallon kafar duniya wato FIFA ya dakatar da shugaban FIFA Joseph Blatter sannan ita kuma kungiyar kwallon kafa ta nahiyar Turai wato UEFA ta dauki irin wannan mataki kan shugabanta Michel Platini. Wata sanarwa da kwamitin da'ar karkashin jagorancin Alkalin Jamus, Hans-Joachim Eckert ta bayar, ta ce an kuma dakatar da babban sakataren FIFA Jérôme Valcke. Hukumar kwallon kafar ta FIFA ta kwashe tsawon shekaru tana fama da badakalar cin hanci da rashawa. Makoni biyu da suka gabata masu shigar da kara na kasar Switzerland sun fara bincike kan Blatter kan aikata laifi cikin har da zargin yin ba daidai ba. Shi ma Platini ana zargisa da karbar makudan kudaden daga Blatter.
Bayan wannan mataki na dakatar da Sepp Blatter daga shugabancin FIFA, yanzu dan kasar Kamaru Issa Hayatou ne shugaban rikon hukumar kwallon kafar ta duniya. Tuni dai Hayatou ya ce ba zai tsaya takarar neman shugabancin hukumar a watan Fabrairun 2016 ba.