1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta daure wani mai sukar gwamnati

Ramatu Garba Baba
December 9, 2022

Kotu a Rasha ta zartas da hukuncin daurin shekaru kimanin takwas da rabi kan dan adawar kasar Ilya Yashin, bayan samun shi da laifin yada labaran karya kan yakin kasar da Ukraine.

https://p.dw.com/p/4KjHK
Ilya YashinHoto: Yury Kochetkov/Pool/AP/picture alliance

A wannan Juma'ar kotu a kasar Rasha ta zartas da hukuncin dauri na shekaru sama da takwas kan wani dan adawar kasar da ta ce, ta kama da laifin yada labaran karya a game da rundunar sojin kasar da ke gwabza yaki da Ukraine. Kotun ta ce, Ilya Yashin ya yi yunkurin bata sunan Rasha a zargin da ya yi ma rundunar sojinta da laifin aikata kisan kiyashi a birnin Bucha ba tare da kwakwarar hujja ba. 

Amma tuni masu sharhi suka danganta wannan al'amari da bita da kullin siyasa, ganin yadda Ilya ke sukar gwamnatin Kremlin kan mamayar makwabciyarta da kuma karfin dangantakarsa da madugun adawar kasar Alexei Navalny. Dama tun bayan kaddamar da yaki a Ukraine a watan Febrairu, Rasha ta samar da dokar hukunta duk wani dan kasar da ya yada labarai na karya a game da aikin da rundunar sojin kasar ke yi.