1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara kada kuri'u a zaben shugaban kasar Masar

May 26, 2014

Tsawon yini biyu ne dai, Misirawa za su kwashe a zaben shugaban kasar da ke gudana, wanda tuni ake ganin dan takara Al-Sissi ne zai yi nasara.

https://p.dw.com/p/1C6pj
Hoto: Mohammed Mahjoub/AFP/Getty Images

A wannan Litinin Misirawa ke kada kuri'a don zaben shugaban kasar da zai maye gurbin zababban shugaba Mohammed Mursi, wanda sojoji suka kifar a bara, a daidai lokacin da ra'ayoyin 'yan kasar ke rabuwa biyu, kan kada kuri'a ko kaurace ma ta. Tuni dai ake ganin cewa tsofon babban kwamandan sojojin kasar Abdel Fattah al-Sissi dan shekaru 59 da haifuwa ne, zai lashe zaben.

Tuni da ma ake ganin tamkar dai shi ne ke jagorancin wannan kasa, tun bayan da ya hambare gwamnatin shugaban kasar Mohamed Morsi, watanni 11 da suka gabata, kuma ya sa aka kulle shi tare da tarin tuhume-tuhume.

Da dama dai daga cikin 'yan kasar ta Masar ke ganin cewa Al-Sissi ne zai iya kawo zaman lafiya a wannan kasa, da ke fama da rigingimu barkatai yau da shekaru uku da suka gabata yayin da wasu kuma ke kallon abokin takarar tashi Hamdeen Sabbahi, a matsayin wani jeka na yika, duk kuwa da cewa ya dage wajan yakin neman zaben da ya gudana a wannan kasa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal