1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara rigakafin corona a Aljeriya

Ahmed Salisu
January 30, 2021

A wannan Asabar din ce Aljeriya ta kaddamar da shirin allurar rigakafin COVID-19, a yankin da cutar ta fi tsananta.

https://p.dw.com/p/3ocCE
Russland Corona-Pandemie | Impfstoff Sputnik V
Hoto: Sergei Bobylev/TASS/dpa/picture alliance

Ministan lafiya Abderrahmane Benbouzid ne ya kaddamar da allurar a gundumar Bilda da ke kusa da Algiers. Sanarwar kamfanin dillancin labarai na APS ya rawaito cewar babban jamin kula da lafiya na gundumar, ya kasance mutum na farko da aka yi wa rigakafin wanda dama can aka tsara fara yinsa ga jami'an kiwon lafiya da tsofaffi da wadanda ke da rashin lafiya masu hadari.

Wannan kasa da ke yankin Arewacin Afirka ta fara yin allurar ne yini guda bayan samun rukunin farko na magungunan mai suna Sputnik V. daga kasar Rasha. Aljeriyar mai yawan al'umma kusan milyan 44, na da masu corona sama da dubu 100 kuma daga cikin wannan adadi fiye da dubu biyu sun rasu.