Sakamakon farko na zaben shugaban kasa a Togo
April 27, 2015Talla
Sakamakon farkon dai na nuni da cewa Gnassingbe da a yanzu haka ke kan karagar mulkin kasar na kan gaba da kaso 62 cikin 100 na kuri'un da aka kada yayin da abokin hamayyarsa Jean-Pierre Fabre ke da kaso 32 cikin 100. Hukumar zaben kasar mai zaman kanta wato CENI ce ta bayyana hakan bayan da aka kirga kaso 12 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben da ya gudana a karshen mako. 'Yan takara biyar ne dai suka fafata a zaben shugaban kasar ta Togo. A shekara ta 2005 ne aka zabi Faure Gnassingbe a matsayin shugaban kasar inda mutane kimanin 500 su ka rasa rayukansu a sakamakon rikicin da ya biyo bayan zaben, kana an sake zabensa karo na biyu a shekara ta 2010 sai dai ba a samu wani tashin hankali ba.