An fara shara'ar harin jaridar Charlie Hebdo
September 2, 2020A ranar Larabar nan ne a birnin Paris na kasar Faransa aka fara sauraren shara'ar mutane 14 da ake zargi da hannu a hare-haren ta'addancin a gidan jaridar nan ta Charlie Hebdo da wasu shagunan Yahudawa cikin tsauraran matakan tsaro. Wadanda ake zargin an shigo d asu Kotun ne da kyalle rufe da fuskarsu, inda aka chajinsu da ta'addanci ko kuma taimaka wa 'yan ta'adda.
Jaridar ta Charlie Hebdo ta yi zanen barkwanci na batanci ga Annabi Muhammadu (S.A.W) shekaru kusan 5 da suka gabata, wanda hakan ya yi sanadiyar salwantar rayukkan mutane sama da 250 wadanda ba su ji ba basu gani ba a hannun wasu mutane da ke goyon bayan ayyukan kungiyar IS.
Richard Malka wanda ya zo kare wani da abin ya rutsa da shi cewa ya yi ''Tabbas yau rana ce da nake tunawa da abokina wanda abin ya rutsa da shi, kuma rana ce da ku 'yan jarida za ta baku damar gudanar da ayyukanku yadda ya dace.''