An fara taron Berlin kan rikicin Libiya
January 19, 2020Talla
Shugabannin kasashe musamman wadanda ake ganin ke goyon bangaren tawaye da Khalifa haftar ke jagoranta, sun fara taron ne a Berlin fadar gwamnatin Jamus.
Sai dai fa jagoran gwamantin da duniya ta amince da ita a Libiyar Fayez al Sarraj, na dora ayar tambaya kan ajendojin Khalifa Haftar, tun ma kafin a fara taron.
Taron na birnin Berlin kamar yadda aka nunar, na da burin kawo karshen takaddamar ne tare ma da hana shigar da makamai a Libiya.
Rikicin siyasa dai ya barke ne a Libiya a shekara ta 2011, matsalar da ta kai ga kisan tsohon Shugaba Moamar Ghaddafi.