1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

An fara taron fatan dakatar da yaki a Ukraine

October 28, 2023

An fara tattaunawar neman zaman lafiya da Ukraine ke goyon baya a tsibirin Malta, inda bayanai ke tabbatar da halartar wakilai daga kasashen duniya sama da 50.

https://p.dw.com/p/4Y9jj
Shugaba Vlodymyr Zelenskyy na Ukraine
Shugaba Vlodymyr Zelenskyy na UkraineHoto: Virginia Mayo/AP Photo/picture alliance

Yayin zaman taron na kwanaki biyu da za a yi, Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar Ukraine na fatan samun goyon bayan da zai kai ga kawo karshen yaki da Rasha ta kaddamar a kan kasarsa a bara.

Sai dai duk da alamun samun goyon baya da Ukraine din ke fata, daga gefe guda Amurka ta dakatar da ba ta agajin sabbin makaman yaki.

Daga nata bangare kasar kasar Rasha ta yi watsi da taron da ta ce na makiyanta ne zalla kuma ta bijire masa.

A farkon wannan shekarar ne dai aka yi makamancin taron a birnin Jeddah na Saudiyya da kuma Copenhagen na kasar Denmark.