An fara taron koli na kungiyyar OPEC
November 17, 2007Talla
An fara taron ƙolin shugabannin ƙasashen ƙungiyyar OPEC, ta ma su arziƙin man fetur,a birnin Riyadh na ƙasar Saudiya.Taron yazo ne a dai dai lokacin da ƙasashen ke fuskantar matsin lamba,na ƙara yawan man da su ke samarwa a kasuwarsa ta Duniya. Koda a jiya ministocin man ƙasashen na Opec 12, sun tattauna irin ajandojin da wannan taro na yau zai yi baje koli kansu. Daga cikin su, akwai bukatar duba yadda darajar Dola take ƙara faɗuwa. Ƙasashen na OPEC dai na hada hadar sayar da man ne ta hanyar amfani da Dolar. Har ilya yau taron zai kuma duba yiwuwar sa rangwame ga hada- hadar man ga matalautan ƙasashe.Taron da za a shafe kwanaki biyu ana gudanarwa, zai kuma duba batu na inganta harkoki na muhalli.