1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun nukiliyar Iran a taron Majalisar Dinkin Duniya

September 25, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump ya soki lamirin gwamnatin kasar Iran, inda ya zarge ta da haddasa rudanin da ke haddasa barna lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya (MDD) na shekara-shekara.

https://p.dw.com/p/35UHC
US-Präsident Trump spricht vor der Generalversammlung der Vereinten Nationen in New York
Hoto: Reuters/C.Allegri

Shugaban na Amirka da ke jawabin bude taron koli na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) karo na 73 a birnin New York na kasar ta Amirka, inda ya kare matsayinsa na bijire wa yarjejeniyar nukiliyar Iran da ya yi a baya.

Shugaban na Amirka Donald Trump dai ya fara ne da bayyana abin da ya ce nasarori ne da Amirkar ta samu cikin shekaru biyu da ya yi na jagoranci, abin da ya ce kasar ba ta gani ba a tarihinta.

US-Präsident Trump spricht vor der Generalversammlung der Vereinten Nationen in New York
Hoto: Reuters/S.Stapleton

Sai dai shugabanni da wakilan na duniya da ke taron sun kwashe da dariya lokacin da yake wannan ikirarin, da ya kai shi ga cewa bai yi tsammanin martanin daga gare su ba.

Dangane da kasar Iran, Shugaba Trump ya ce shugabanninta na kwashe dukiyar kasar, tare da cewa tana daukar nauyin ta'addanci a ketare. Ya kuma yi kiran kasashen duniya da su kaurace wa Iran, muddin ta ci gaba da manufofin da take a kansu.

Shugaban na Amirka ya kuma yaba ci gaba da aka samu tsakanin kasarsa da Koriya ta Arewa cikin ‘yan watannin baya, ci gaban da ya ce ya kai ga kwance damarar makamai masu linzami da ake fargabar Koriya ta Arewa a kansu.

Ya ce ''Manyan makamai masu linzami sun daina tashi ta ko'ina da ake gani a baya. Gwaje-gwajen nukiliya ma sun tsaya, wasu daga cikin cibiyoyin gwaje-gwajen ma tuni aka rusa su. Ina mika godiya ga Shugaba Kim Jong Un kan matakan da ya dauka duk da cewar da sauran aiki a gaba.'' 

USA New York - 73. UN Generalversammlung - Pakistans Außenminister Shah Mehmood Qureshi
Hoto: Pakistan Embassy/Washington

Yayin da Shugaba Trump ke karfafa batu na martabar Amirka, shi kuwa sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Getteres na cewa ne samun hadin kan kasashe na fusknatar barazana, lokacin kuma da aka fi bukatar hakan:

"Kamar yadda tsohon sakatarenmu Kofi Annan ya taba tunatar da mu a baya, makomarmu guda ce. Kuma muna iya cimmata ne kawai idan muka hada karfi waje guda, kuma hakan ne ya sa muke da Majalisar Dinkin Duniya. Dole ne mu yi gyara kan rashin yarda da juna, dole ne kuma mu karfafa daraja na daidaikunmu da kuma na dukkaninmu jam‘i

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa a taron ya yi kiran a dubi batun yarjejeniyar nukiliyar Iran, abin da ya kama da martini ga kalaman shugaban Amirka, da kuma janyewar da ya yi daga yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2015.

Mr. Macron ya kuma yi bayani kan bukatar bai wa nahiyar Afirka fifiko, ta fuskar tsaro da sauran fannonin na ci gaba, saboda muhimmancinsu ga duniya.

USA New York - Emmanuel Macron trifft auf Hassan Rouhani
Hoto: Getty Images/AFP/L. Marin

Shugaban Turkiyya Racep Tayip Erdogan, ya ja hankalin taron ga matakan da Amirka ta dauka na takunkuminn tattalin arziki a kan Turkiyya, abin da ya ce babu wanda zai so duniya ta fuskanci rudani na arzikin.

Shugaban na Turkiyya, ya kuma bayyana MDD a matsayin kuliyar matar malam, da hanaklinta ya fi karkata ga kasashen duniya biyar wato  Amirka da Rasha da China da Faransa da kuma Birtaniya musamman a kwamitin sulhu.

Ya ce muddin muka amince duniya ta wuce karfin kasashe biyar, to lallai lokacin ne za mu amsa cewa muna kan turbarmu ta mutane da ke mutunta hakkokin juna.

Wannan dai taro ne da za a dauki makonni biyu ana yi, inda bayan shugabannin, wasu manyan jakadun ma za su gudanar da na su.