1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fidda sunayen yan takara a Iran

Usman ShehuMay 22, 2013

Yayinda zaben shugaban ƙasar Iran ke ƙaratowa, an fidda sunayen mutane takwas da za su tsaya takara a zaben shugaban ƙasa da zai gudana a watan Juni dake tafe.

https://p.dw.com/p/18c7i
FILE - This Monday, Aug. 3, 2009 file photo released by the official website of the Iranian Supreme Leader's office, shows Iranian President Mahmoud Ahmadinejad, right, delivering a speech after Supreme Leader Ayatollah Ali Khamenei, seated at left, formally endorsed him for a second term as President during an official ceremony in Tehran, Iran. As Iran's capacity to build nuclear weapons grows, intelligence assessments from nations that follow Tehran's atomic progress discern increasing indecision and squabbling by its leadership on whether to make such arms - and if so, how overtly. Most suggest Ahmadinejad is more circumspect. But an intelligence summary shared recently with The Associated Press sees Supreme Leader Ayatollah Ali Khamenei as the more cautious of the two and says the Revolutionary Guard is benefiting from the dispute, with some of the authority normally exercised by the president devolving to it. (AP Photo/Office of the Supreme Leader, File) ** EDITORIAL USE ONLY, NO SALES ** EDITORS NOTE AS A RESULT OF AN OFFICIAL IRANIAN GOVERNMENT BAN ON FOREIGN MEDIA COVERING SOME EVENTS IN IRAN, THE AP WAS PREVENTED FROM INDEPENDENT ACCESS TO THIS EVENT
Khamenei da AhmadinejadHoto: AP

A ƙasar Iran hukumar tantace yan takaran shugaban ƙasa ta fidda sunayen mutane takwas da za su shiga takaran shugaban ƙasa a zaben wata mai zuwa. Daga cikin sunayen da aka amince musu shiga takara harda Saeed Jalili, wanda yanzu haka shine sakataren tsaron ƙasar Iran, kana shine ke wakiltar kasar Iran a tattaunawar nukilya da ta ke yi da ƙasashen yamma. Wasu da aka soke sunayensu harda tsohon shugaban ƙasar Hashemi Rafsanjani da kuma wani na hannun daman shugaban ƙasar Iran Ahmadinejad wato Esfandiar Rahim Mashaei. Don haka shugaban ƙasar ta Iran Ahmadinejad, yace zai sake tattaunawa da shugaban addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei bisa soke sunan abokin nasa. Koda yake akwai dan uwan shugaba Ahmadinejad, wato Wavud Ahmadinejad wanda ya tsaya takaraqn shugaban ƙasa, amma tuni shugaba Mahmud Ahmadinejad yace zai goyi bayan shugaban ma'aikatar fadarsa a yanzu haka wato Esfandiar Rahim Mashaei. A ranar 14 ga watan juni mai tsayawa ne dai za a gudanar da zaben shugaban ƙasar ta Iran.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu