Jirgi makare da 'yan cirani ya tuntsure a teku
October 7, 2019Sojojin da ke kula da gabar ruwan kasar Italiya, sun ce sun yi kokarin ceto mutanen da rayukansu bayan da suka fuskanci jirgin na cikin garari, amma rashin kyaun yanayi da kuma yadda aka lodawa jirgin fasinjoji fiye da kima ya sa sun fuskanci tarnaki. Magajin garin yankin Toto Martello ya bayyana takaici game da wannan iftala'in da ya ce sam bai dace a bari ya auku ba.
Wannan na zuwa ne mako guda da gudanar da wani taron cika shekaru shida da hadarin jirgin ruwan da ya lakume rayukan 'yan cirani sama da 360 daga cikin 500 da jirginsu ya nutse cikin tekun na Bahar Rum.
Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce rayukan 'yan cirani ko 'yan gudun hijira akalla dubu 19 ne suka salwanta a yayin da suka yi yunkurin shiga Turai daga shekarar 2016 zuwa yanzu.