1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An gano gawarwakin 'yan ci-rani a cikin jirgin ruwa a Spain

October 30, 2023

Sojojin ruwan kasar Spain sun sanar da gano gawarwakin 'yan ci-rani guda biyu a cikin jirgin ruwan da ke dauke da mutane sama da 200, cikinsu har da kananan yara 34, a tsibirin Canary na kasar a Litinin din nan

https://p.dw.com/p/4YCgP
Hoto: Europa Press/ABACA/picture alliance

Sojojin ruwan kasar Spain sun sanar da gano gawarwakin 'yan ci-rani guda biyu a cikin jirgin ruwan da ke dauke da mutane sama da 200, cikinsu har da kananan yara 34, a tsibirin Canary na kasar a yau Litinin.

Karin bayaniFafaroma ya nemi da a taimaka wa 'yan cirani

Wannan dai shi ne jirgin ruwa na uku dauke da 'yan ci-rani daga Afirka da ya isa tsibirin yau, bayan mai dauke da mutane 83 da kuma mai dauke da mutane 95, inda daga ranar 1 ga watan Janairun bana zuwa 15 ga watan Oktoba 'yan ci-rani 23,500 suka isa tsibrin Canary daga Afirka.

Karin bayaniSaudiyya ta bindige 'yan ci-rani

A yau ne dai mai rikon mukamin ministan harkokin cikin gidan Spain Fenando Grande-Marlaska zai kai ziyara Senegal, don tattauna hanyoyin dakile yunkurin tsallakawa zuwa Turai da mutanen ke yi, kasancewar daga nan suka fi fitowa don zuwa Turai.