An gano wagegen kabari a Mali
April 23, 2022Gwamnatin kasar Mali ta ce, ta gano wani kabari makare da gawarwaki a kusa da tsohon sansanin da rundunar Faransa ta mayar wa gwamnatin kasar ikonsa kwanaki hudu da suka gabata a yankin Gossi da ke arewacin kasar.
Sai dai sanarwar na zuwa ne 'yan sa'oi bayan da rundunar Barkhane ta Faransa da aka tsugunar a kasar ta ce, ta nadi wani bidiyo na sojojin hayan Rasha suna binne gawarwaki a kusa da sansanin don shafawa rundunar Faransan kashin kaji.
Kamfanin Dillancin labaran AFP ya ce, ya ga bidiyon da aka yi amfani da kirar jirgi mai sarrafa kansa da ya nuna wasu sojoji suna kokarin rufe gawarwaki da yashi a kusa da sansanin da ke Gossi.
Gwamnatin Mali ta kaddamar da binciken gano hakikanin gaskiyan lamarin. A hukumance Faransa ta mika wa sojojin Mali iko da sansanin na Gossi a ranar Talatar da ta gabata a wani bangare na mutunta yarjejeniyar janyewar da aka sanar a watan Febrairu.