An gano masu ɗauke da cutar Ebola a Laberiya
March 31, 2014Talla
Hukumar ta ce mutanen guda biyu waɗanda aka gano suna ɗauke da ƙwayoyin cutar, suna zaune ne a ga garin Foya da ke kan iyaka da Guinea da kuma Saliyio. Cutar wacce ta ɓulla a cikin farkon wannan wata a Guinea Conakry inda ta kashe mutane 70. Manazarta al'amuran kiwon lafiya na cewar tana da alamar bazuwa a cikin sauran ƙasashen yankin yammaci Afirka.
Tuni dai da Ƙasar Senegal ta rufe kan iyakarta da Guinea ,tare da haramta cin wasu kasuwannin ƙayukan ga jama'ar ƙasar da ke kan iyakar ƙasashen biyu.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar