1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano wasu sinadarai masu kashe cutar Zika

Gazali Abdou TasawaJune 23, 2016

Wasu kwararrun likitoci na Turai sun sanar da gano wasu sinadarai masu karfi na garkuwar jikin dan Adam da ke iya kashe kwayar cutar Zika.

https://p.dw.com/p/1JCAl
Zika Virus
Hoto: Reuters/I. Alvarado

Rahoton Kwararrun likitocin da suka hada da na cibiyar bincike ta Pasteur da kuma Kwalejin Imperial ta Landan wanda aka wallafa a wannan Alhamis ya bayyana cewar a wani gwajin da likitocin suka gudanar, sabbin sinadaren garkuwar jikin dan Adam din da suka gano sun yi nasarar kashe kwayar cutar Zika dama ta Dengue.

Kuma wannan ci gaba da aka samu zai taimaka sossai wajen kirkiro da allurar maganin cututtukan biyu.Wani sakamakon bincike na daban da aka wallafa a wannan Alhamis ya nunar da cewar akwai yiwuwar yaduwar annobar cutar Dengue a yankin Latin Amirka ita ta taimaka ga yaduwa annobar cutar Zika da aka fuskanta a yankin a baya bayan nan, domin kwayoyin cututtukan biyu na da dangataka sossai da juna ta hanyar nau'in sabro daya.