1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gargadin Rasha kan rikicin siyasar Ukraine

March 14, 2014

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce kasashen duniya za su maida kakkausar martani ga Rasha in ba ta daina dagula rikicin siyasar Ukraine ba.

https://p.dw.com/p/1BQ7T
Russland Präsident Wladimir Putin
Hoto: REUTERS

Mr. Kerry ya bayyana hakan ne bayan da ya shafe tawon sa'o'i shidda ya na ganawa da takwarsa na Rasha Sergei Lavrov, inda ya kara da cewar Amurka da sauran kasashen dunyia ba za su amince da sakamakon kuri'ar raba gardamar da za a kada ba kan ballewar yankin Kirimiya daga kasar Ukraine.

A daura da wannan kuma kungiyar tsaro ta NATO ta ce kuri'ar ta raba gardama da za a yi kan ballewar Kirimiya karen tsaye ne ga kundin tsarin mulkin Ukraine kazalika hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa, sai dai shugaban Rasha Vladmir Putin a wata zantawa da ya yi da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ce hakan bai sabawa doka ba kuma za a gudanar da kuri'ar kamar yadda aka tsara.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Pinado Abdu-Waba