An gaza cimma matakan diplomasiya a Siriya
September 23, 2016Masu shiga tsakani daga bangaren Majalisar Dinin Duniya, sun yi amfani da taron koli da Majaliasar ta Dinkin Duniya ta shirya a birnin New York na Amirka don tattaunawa ta musamman da nufin samo sabbin dabaru na kulla sabon yarjejeniyar tsagaita wuta a kasar da ya ruguje sakamakon barin wuta tsakanindakarun gwamnati da bangaren 'yan tawaye.
Gabannin kammala taron dai, an dora laifi ga dukkanin bangarorin da ke fafatwa a rikicin na Siriya. Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Staffan de Mistura, ya bayyana takaicin yadda taron ya gaza cimma matsaya da zai sauwake wahalar da 'yan Siriya ke fama da ita shekara da shekaru. Wannan dai na zuwa ne bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta cimma nasarar shigar da kayan agaji a Damascus tun bayan da wani ayarinta ya fuskanci hari a ranar Litinin din da ta gabata.