An girka sabuwar gwamnatin rikon kwarya a Falasdinu
February 6, 2012Kungiyoyin da ke hammaya a Falasdinu, wato Fatah da Hamas sun amince su girka gwamnatin rikon kwarya, karkashin jagorancin shugaba Mahmud Abbas. Shugaban zai jagorancin gwamnatocin da ke yamma da gabar tekun Jordan da kuma zirin Gaza kamar yadda wani babban jami'i wanda ya wakilci gwamnatin ya bayyana, bayan tattaunawar da kungiyoyin suka gudanar a Katar. Ana sa ran a 'yan watanni masu zuwa kungiyoyin na Fatah da Hamas zasu kuma sake amincewa da jadawalin gudanar da zaben Majalisar dokoki da na shugaban kasa. Tun a bara Kungiyoyin biyu suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar sulhu tsakaninsu wacce kuma ta tanadi kawo karshen aiwatar da ayyuka karkashin gwamnatoci biyu, kamar yadda suka rika yi a daa, wato Fatah na jagorantar gabar yamma da tekun jordan a yayinda ita kuma Hamas ke jagorantar zirin Gaza. Wannan rabuwan kai tsakanin kungiyoyin na daya daga cikin abubuwan da suka kawo tsaiko a yarjejeniyar sulhun yankin da Israila.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Saleh Umar Saleh