An gudanar da sallar Jumma'a a Hagia Sofia
July 24, 2020Talla
Dubban mutane ciki har da shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyip Erdogan da ya samu rakiyar ministan kudi na kasar da ke zama sirikinsa suka hallarci sallar jumma'ar, albarkacin gwagwarmayar da al'ummar kasar masu kishin addini Islama suka kwashe tsawon lokaci suna yi.
Wannan mataki dai na zuwa ne bayan da wata kotu a birnin ta yanke hukuncin mai da ginin Hagia Sofia zuwa masallaci. Ra'ayoyi sun banbanta a ciki da wajen kasar tun bayan wannan hukunci. Tuni hukumar raya ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO ta nuna rashin jin dadi kan matakin mayar da wanann ginin tarihi zuwa masallaci.