1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gudanar da shagulgulan Sallah Karama a Nijar

May 23, 2020

Musulmi a Jamhuriyar Nijar, sun gudanar da karamar Sallah a yau Asabar, sabanin yadda wasu kasashen duniya ke cewa Lahadi ce ranar da za a yi.

https://p.dw.com/p/3cfTz
Eid Al Fitr in Zinder, Niger
Hoto: DW/L. Malam Hami

Bayan sanar da ganin jaririn wata da hukumomi suka yi a kasar ne dai al'umar Musulmin na Jamhuriyar Nijar suka tashi a yau Asabar a matsayin ranar ta Sallah karama.

Majalisar Musulmin kasar ta ce an ga watan a garuruwan Magaria a yankin Damagaram da kuma Maine_soroa da N'guiguimi da kuma N'Gourti da ke Diffa.

A cewarta yau Asabar ce ranar 1 ga watan Shawwal, saboda haka Azumi ya zo karshe ke nan a jiya Juma'a 29 ga watan Ramadan.

Hakan kuwa ya zo ne yayin da Saudiyya da wasu kasashen ke cewa a gobe Lahadi ne za a gudanar da bukukuwan Sallar Azumin, saboda rashin ganin watan na Shawwal.

Da hantsin yau Asabar ne dai aka gudanar da hawan Idi a yankin Damagaram inda Sultan Abubakar Sanda, ya yi wa Musulmin yankin da kewaye fatan katari da alheran da ke kunshe cikin watan Azumi da aka kammala. Ya kuma bukaci jama'a su dage da addu'o'in neman kawo karshen annobar da duniya ke a ciki.